ha_tn/gen/20/04.md

1.3 KiB

Yanzu ... ce

Ana amfani da wannan kalmar wajen sa alamar canja labari zuwa bayani game da Abimelek. (Duba: rc://*/ta/man/translate/writing-background)

Abimelek kuma bai kusance ta ba

Wannan wani hanyar cewa ne bai yi jima'i da ita ba. AT: "Abimelek bai kwana da Sarai ba" ko "Abimelek bai taba Sarai ba" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-euphemism)

har ma al'umma mai adalci

"al'umma" a nan na nufi mutanen ne. Abimelek ya damu cewa ba shine kadai Allah zai hukunta ba, har da mutanen sa. AT: "har ma da mutanen da basu da laifi" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

ba shi da kansa ne ya ce da ni 'ita 'yar'uwataba ce?' Har ma ita da kanta ta faɗa, cewa 'Shi ɗan'uwana ne'

Wannan yana da ambato cikin zance. Ana iya bayyana su azaman maganganun kai tsaye. AT: "ba shi da kansa ne ya ce da ni wai 'ita 'yar'uwarsa ba ce? Har ita ma kanta ta ce shi ɗan'uwanta ne" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-quotesinquotes]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-quotations]])

Na yi wannan bisa nagartar zuciyata, da kuma rashin laifofin hannuwana

Anan "zuciya" na nufin tunaninsa ko ƙudurisa. "hannu" kuma na nufi abun da ya aikata. AT: "Na aikata wannan da nufin mai kyau" ko "Na yi wannan ba tare da nufin aikata mugunta ba" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)