ha_tn/gen/19/12.md

869 B

Sai mutanen suka ce

"Sai mutane biyun suka ce" ko "Sai mala'iku suka ce"

Ko kana da wani naka a nan?

"Akwai wani da ke na gidanka kuma a cikin birnin?" ko "Kana da wani ɗan iyalinka a wannan wurin?"

duk wanda ka ke da shi a cikin birnin

"wani daga iyalinka da ke zama a birnin"

mu na gab da hallakar

Wannan kalmar "mu" na nufin mala'ikun ne su biyu kadai zasu hallakar da birnin, ba tare da Lot ba. Idan harshenku na da yadda za a iya bayana haka, to a yi amfani da shi a nan. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-exclusive)

zargin da ake yi wa birnin a gaban Yahweh ya yi yawa

Ana iya canja kalmomin nan ta wani hanya domin a bayana kalmar "zargi." AT: "mutane da yawa sun kawo kuka cewa mutanen birnin nan na aikata mugunta" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-abstractnouns) da kuma yadda aka fassara waɗannan kalmomin a Farawa 18:20