ha_tn/gen/19/01.md

1016 B

Mala'ikun guda biyu

A Farawa 18 an bayana cewa mutane biyu sun tafi Spdom. A nan a bayana mana cewa mala'iku ne. (Duba: Farawa 18:22)

a ƙofar Ssodom

"hanyar shigar birnin Saduma." Akwai ganuwa kewaye da birnin, lalle ne mutane su bi ta ƙofar kafin su shiga. Wannan muhimmin wurin ne a birni. Muhimman mutane ne suke zama a wurin.

sunkuyar da fuskarsa har ƙasa

Ya sa gwiywar sa a ƙasa, sai goshinsa da hancinsa kuma na ƙasa.

shugabannina

Wannan kalmar bangirma ne da Lot ya ba wa mala'ikun.

Ina roƙon ku da ku biyo ta gidan baranku

"Na roƙe ku, ku tsaya a gidan bawanku"

wanke ƙafafunku

Mutanen na son wanke ƙafafunsu bayan tafiya.

zamu je mu kwana

Lokacin da mala'ikun suna magana, suna magana game da su biyu ne ba tare da Lutu ba. Su biyun sun shirya su kwana a kwararo. Wasu harsuna na iya amfani da "mu" a nan. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-exclusive)

Kwararo

Wannan a nufi filin gari ne, na jama'a.

su ka tafi tare da shi,

"suka juya su tafi tare da shi"