ha_tn/gen/18/16.md

1.4 KiB

ya raka su a kan hanyarsu

"ya sa su a hanyarsu" ko " domin ya yi bankwana da su". Ya kasance mai ladabi a ɗan yi nisa tare da baƙi yayin da suke barin.

Ko zan ɓoye wa Ibrahim abin da zan aikata ... shi?

Allah yayi amfani da tambaya a nuna cewa zai yi wa Ibrahim magana game da wani muhimmin abu, kuma zai fi kyau ya yi haka. AT: "Bai kamata in ɓoye wa Ibrahim abin da na ke shirin yi ba, kuma ba zan ɓoye ba ... shi." ko " Ya kamata in faɗa wa Ibrahim abin da na ke shirin yi, kuma zan faɗa ma shi... shi" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

dukkan al'uman duniya za su sami albarka ta wurinsa

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "Zan albarkaci dukka al'uman duniya ta wurin Ibrahim" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

domin ya koya

"cewa zai shiryar" ko "don ya umarta"

su bi tafarkin Yahweh ... domin Yahweh ya cika ... da ya faɗa

Yahweh na magana game da kanshi kamar wani ne dabam. AT: "domin kiyaye abin da ni, Yahweh na ke so ... Ni, Yahweh, zan kawo ... na faɗa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-123person)

su aikata adalci da aikin adalci

Wannan na faɗin yadda za a kiyaye hanyar Yahweh.

domin Yahweh ya cika abin da ya faɗa wa Ibrahim zai aikata a gare shi

"domin Yahweh ya albarkace Ibrahim kamar yadda ya ce zai yi." Wannan na nufin alkawarin albarkar Ibrahim na mayar da shi babban al'uma.