ha_tn/gen/15/14.md

991 B

Muhimmin Bayani:

Yahweh ya ci gaba da yi wa Ibram maganar sa'ad da Ibram yana cikin mafarkin.

Zan hukunta

Anan "hukunta" na nufin abin da zai faru bayan Allah ya yi shari'a. AT: "Zan azabtar" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

mallaka mai yawa

Wannan karin magana ne. AT: "mallaka mai matuƙan yawa" ko "wadatar dukiya" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

za ku je wurin ubanninku

Wannan wata hanya ɗabi'a ne na cewa "za ku mutu." (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-euphemism)

za a yi maku jana'iza a shekaru ma su kyau

"za ku tsufa kafin ku mutu, iyalinku kuwa su yi muku jana'iza"

A cikin tsara ta huɗu

Tsara ɗaya a nan na nufi tsawon shekaru ɗari. "bayan shekaru ɗari huɗu"

za su sake zuwa nan

"zuriyarka za su sake dawo nan." Zuriyar Ibrahim za su sake komowa ƙasar da Ibram ke zama, da kuma ƙasar da Yahweh ya alkawatar ma sa.

bai kai matsayinsa ba tukuna

"bai cika ba" ko "sai ya yi muni kafin zan hukunta su"