ha_tn/gen/12/01.md

1.1 KiB

To yanzu

Ana amfani da wannan kalmar domin nuna alamar sabon sashin labari.

Ka tashi ka bar ƙasarka da danginka

"Ka tafi daga ƙasarka, daga iyalika"

zan maishe ka babbar al'umma

"ka" a nan na nufin Ibram ne, amma Ibram na wakiltar zuriyar sa. AT: "Zan fara babbar al'umma ta wurin ka" ko "Zan mai da zuriyarka babbar al'umma" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)

kuma sa sunanka ya yi girma

Kalmar "suna" tana wakiltar mutuncin mutum. AT: "kuma maishe ka shaharare" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

za ka zama albarka

An fahimci waɗannan kalmomin "zuwa wasu mutane." AT: "za ka zama albarka ga wasu mutane" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-ellipsis)

duk wanda ya rena ka, zan la'anta shi

"zan la'anta duk wanda ya rena ka" ko "idan wani ya mayar da kai abin banza, zan la'ance shi"

Ta wurin ka dukkan al'ummar duniya za ta sami albarka

Ana iya sanya wannan aiki. AT: "Zan albarkace al'umman duniya dukka ta wurin ka" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

Ta wurin ka

""Saboda ka" ko "Domin na albarkace ka"