ha_tn/gen/08/20.md

1.0 KiB

gina bagadi ga Yahweh

"gina bagadi, ya keɓe wa Yahweh" ko "gina bagadin sujada ga Yahweh." Mai yiwuwa ya gina shi da duwatsu ne.

dabbobi ma su tsarki ... tsuntsaye ma su tsarki

"tsarki" a nan na nufin cewa Allah ya yarda a yi amfani da waɗannan dabbobin domin hadaya. Ba a amfani da wasu dabbbobi wajen miƙa hadaya, ana kiran su "mara tsarki."

miƙa hadaya ta ƙonawa

Nuhu ya kashe dabbobin, sai ya ƙona su kurmus a matsayin baiko ga Allah. AT: "ƙona dabbobin a matsayin baiko ga Yahweh"

ƙanshi mai gamsuwa

Wannan na nufin ƙanshi mai kyau daga gasashen nama.

nufe nufen mutum a zukatansu mugunta ne tun daga yarintakarsu

"tun daga farkon shekarunsu, sun kasnace da nufin aikata mugunta" ko "tun suna ƙuruciya, suna son aikata mugayen abubuwa"

Muddin duniya tana nan

"muddin jurewa duniya" ko "muddin kasancewa duniya"

lokacin shuka

"lokacin da ake yin shuki"

sanyi da zafi, damina da rani

Wannan maganar na nufin yanayi lokaci biyu da suke a shekara. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-merism)