ha_tn/gen/08/13.md

1.3 KiB

Sai ya zamana

Ana amfani da wannan maganar domin ba da alama na farkon wani sabon sashin labarin. Idan harshenku na da wani hanya faɗin haka, ana iya yanke shawarar amfani da shi a nan.

a shekaru na ɗari shida da ɗaya

"sa'ad da Nuhu na shekara 601" (Duba: rc://*/ta/man/translate/translate-ordinal)

a wata na farko, a ranar farko

Domin Musa ne ya rubuta wannan littafi, mai yiwuwa ana nufin watan farko na kalandar Ibraniyawa ne, amma ba tabbacin wannan. (Duba: [[rc:///ta/man/translate/translate-hebrewmonths]] da [[rc:///ta/man/translate/translate-ordinal]])

ruwa ta bushe daga ƙasa

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki AT: "ruwan da ya rufe ƙasa ya bushe" ko "iska ta busher da ruwan da ya rufe ƙasa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive).

rufin jirgin ruwan

Wannan na nufin abin da aka sa domin hana ruwan sama shiga cikin jirgin.

ga shi

Kalmar "ga shi" na jawon hankalin mu ne ga muhimmin sakon da ke zuwa nan gaba.

A cikin wata na biyu, a ranar ashirin da bakwai

"rana ta ashirin da bakwai ga watan biyu." Wannan mai yiwuwa ana nufin wata na biyu na kalandar Ibraniyawa ne, amma ba tabbacin wannan. (Duba: [[rc:///ta/man/translate/translate-hebrewmonths]] da [[rc:///ta/man/translate/translate-ordinal]])

ƙasa ta bushe

"ƙasar ta bushe gaba ɗaya" (UDB)