ha_tn/gen/07/11.md

1.3 KiB

Muhimmin Bayani:

Ayoyi 6-12 na maimaita sau na biyu ne da kuma ba da bayyani filla-filla game da yadda Nuhu ya shiga jirgin da iyalinsa da kuma dabbobin a cikin 7:1. Wannan ba sabon aukuwa ba ne.

a cikin shekara ta ɗari shida na rayuwar Nuhu

"A sa'd da Nuhu na shekaru 600" (UDB) (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-ordinal)

A ranar sha bakwai ga watan biyu

Tun da shike Musa ne marubucin wannan littafi, ya yiwu yana nufin wata na biyu a kalanda Ibraniyawa, amma ba a tabbatar da wannan ba. (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/translate-hebrewmonths]] and [[rc:///ta/man/translate/translate-ordinal]])

a wannan ranar

Wannan na nufin takamamen ranar da ruwan ta fara. Wannan maganar na nanata yadda waɗannan abubuwan suka faru nan da nan a sa'ad da lokaci ya kai.

maɓuɓɓugai na manyan zurfafa suka fashe

"ruwayen karkashin duniya suka gaggauto zuwa farfajiyar saman duniya"

manya zurfafa

Wannan na nufin teku da ake tsammanin na karkashin duniya.

tagogin sama suka buɗe

Wannan na nufin ruwan sama. Wannan na bayana sararin sama kamar rufi ne da ke hana ruwan da ke sama daga saukowa a duniya. A sa'ad da tagogi ko kofofin da sararin sama suka buɗe, sai ruwa ta sauko ta cikin su. AT: "sararin sama ta buɗe" ko "kofofin sama suka buɗe"

ruwan sama

Idan harshenku na da kalma wa ambaliyan ruwa, zai dace a nan.