ha_tn/gen/07/08.md

957 B

Muhimmin Bayani:

Ayoyi na 6-12 sun maimaita a karo na biyu kuma suna ba da ƙarin haske game da yadda Nuhu ya shiga cikin jirgi tare da iyalinsa da dabbobin a cikin Farawa 7: 1-5. Wannan ba sabon abu bane.

dabbobi masu tsarki

Waɗannan dabbobi ne da Allah ya yaddar wa mutanen sa su ci, su kuma mika masa hadaya

dabbobi marasa tsarki

Wannan dabbobi ne da Allah baya yaddar wa mutane sa su ci ba ko su yi hadaya da su.

biyu-biyu

Dabbobin suka shiga jirgin biyu-biyu, na miji da ta mace.

Ya zama sa'ad da

Ana amfani da wannan maganar domin a ba da alama ne a cikin labarin: farin ambaliyan. Idan harshenku na da hanya yin wannan, ana iya yin amfani da shi a nan.

bayan kwanaki bakwan

"bayan kwanaki bakwai"

ambaliyan ruwan ya sauko bisa duniya

Bayyanin wannan maganar a fili shi ne, "aka fara ruwan sama" (UDB). AT: "aka fara ruwan sama, ambaliyan ruwan kuwa ya sauko bisa duniya" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)