ha_tn/gen/03/22.md

1.6 KiB

Mutumin

Mai yiwuwa ana nufi 1) Allah magana game da mutum ɗaya ne, na mijin, ko 2) Allah na magana game da mutane dukka, wato na miji da matan shi. Ko da mutum ɗaya ne Allah ke magana da, abin da ya faɗa ya shafe su dukka biyu.

kamar ɗayan mu

"kamar mu." Wakilin sunan nan "mu" jam'i ce. Duba yadda aka juya "Bari mu yi" a Farawa 1:26.

sanin nagarta da mugunta

Anan "nagarta da mugunta" ƙarin magana ne da ke nufin iyakar farko da karshen kowani abu da duk abin da ke tsakani. Dubi yadda aka juya "sanin nagarta da mugunta" a cikin Farawa 2:9. AT: "sanin komai, da nagarta da mugunta" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-merism)

kada a yarda mi shi

Ana iya bayyana wannan ta hanyar aiki. AT: "ba zan yarda mi shi ba" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

itacen rai

"itace da ke ba da rai."

ƙasar, inda aka ɗauko shi

"ƙura, dommin daga ƙura ya fito." Wannan baya nufin wani takamamen ƙasa ne da Allah a ɗauko mutumin.

domin haka Allah ya fisshe shi daga cikin gonar

"Allah ya tilasta mutumin ya bar cikin gonar." Wannan na bayana abin da ya faru a Farawa 3:22, inda ya ce " Allah Yahweh ya kori mutumin daga gonar Aidan." Ba wai Allah ya kori mutumin na biyu ba ne.

ya nome

Wannan na nufin yin aikin da a ake bukata domin amfanin gona ta girma da kyau. juya wannan kamar a 2:4.

domin tsare hanya zuwa itacen rai

"domin ya tsayad da mutane daga zuwa itacen rai"

takobi mai harshen wuta

Mai yiwuwa ana nufi 1) takobi da ke da harshen wuta akai, ko 2) harshen wuta da kamar siffar takobi. harsuna da ba su da takobi na iya amfani da makami kamar mashi.