ha_tn/gen/03/17.md

1.6 KiB

Adamu

Adamu da "na miji" na da kalma ɗaya ne a harshen Ibraniyanci. Wasu juya na amfani da "Adamu" wasu kuma "na mijin." Ana iya amfani da kowane domin ana nufin mutum ɗaya ne.

ka kasa kunne ga muryar matarka

Wannan ƙarin magana ne. AT: "ka yi biyayya da abin da matar ka ta faɗa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

ka ci daga itacen

Ana iya faɗin abin da suka ci. AT: "ci daga 'ya'yan itacen" ko "ci daga wasu 'ya'yan itace" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

a la'antar da ƙasa

Kalmar "la'anta" na zuwa a farkon maganar domin a jadada cewa, ƙasar da Allah ya ce na kyau a baya, na karkashin la'ana yanzu. AT: "Ina la'antar ƙasa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

ta wahalar aiki

"ta wurin aiki tuƙuru"

za ka ci daga cikinta

Kalmar "ta" na nufin ƙasa ne, kuma yana bayana sashin amfanin gona da ke girma a cikin ƙasa da mutane ke ci. AT: "za ka ci daga abin da ya girma a cikinta" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

tsire-tsiren jeji

Mai yiwuwa ana nufi 1) "tsire-tsiren da ka ke nomar ta a gonar ka" ko 2) "tsire-tsiren da ke girma a filin jeji."

Da zuffar fuskar ka

"Za ka yi zuffa da aiki tuƙuru"

za ka ci gurasa

Anan "gurasa" na nufi kowani irin abinci. AT: "za ka ci abinci" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)

har ka koma ƙasa

"har mutuwarka, a kuma sa jikin ka a cikin ƙasa." Wasu al'adu na sa jikin wanda suka mutu a rami a cikin ƙasa. Wahalar aikin mutum ba ta karewa har sai lokacin mutuwarsa da biso.

gama turɓaya ka ke, kuma turɓaya za ka koma

"Da turɓaya ne na yi ka, haka kuma jikin ka zai zama turɓaya."