ha_tn/gen/03/14.md

1.6 KiB

kai kaɗai la'ana za ta bi

"kai kaɗai aka la'anta." Kalman "la'anta" ya fito a farkon maganar a harshen Ibraniyanci domin jadada bambancin albarkan da Allah ya sa wa dabbobin da wannan la'anta da ke akan macijin. Haka aka "saba la'anta", ko yadda ake faɗin kalmar la'antawa. Ta ambacin wannan la'ananci, Allah ya sa haka ya faru.

dukkan dabbobin gida da na jeji

"duk dabbobin da ake kiwo a gida da na jeji"

rubda ciki za ka yi tafiya

"da ciki za ka dinga tafiya a ƙasa." Maganar "da cikin ka" ya zo a farkon maganar domin a jadada bambanci tsakanin yadda sauran dabbobi za su yi tafiya da kafafunsu amma macijin kuwa rub da ciki zai yi. Wannan na yadda a ka saba la'anta ne.

turɓaya za ka ci

"ƙura za ka ci." "Turɓaya ne" ya zo a farkon maganar domin nuna bambancin tsire-tsire da sauran dabbobi za su ci da kuma datti da ƙurar da ke ƙasa da macijin zai ci. Wannan ma na yadda aka saba la'anan ne.

ƙiyayya tsakaninka da matar

Wannan na nufin cewa macijin da macen za su zama abokan gãba.

zuriya

Kalmar "zuriya" na nufin abin da na miji ya ke sa a cikin mace domin yaro ya girma a cikin ta. yadda kalmar yake, ya na iya nufin mutum ɗaya ne ko fiye. A nemi kalmar da zai iya bayana zuriya na iya zama ɗaya ko fiye ɗaya.

shi zai ƙuje ... diddigensa

Kalmar "shi" da "sa" na nufin zuriyar matar. Idan kalmar "zuriya" na jam'i ne, ana iya juya shi haka "za su ƙuje ... diddigensu"; in ya kasance haka, ana iya sharihinta cewa "su" wakilin suna ne da nufin mutum ɗaya. (Dubai: rc://*/ta/man/translate/figs-pronouns)

ƙuje

"murkushe" ko "boga" ko "farmaki"