ha_tn/gen/02/04.md

1.3 KiB

Muhimmin Bayani:

Sauran Farawa sura biyun na magana game da yadda Allah ya halicci mutane a cikin kwana na shida.

Waɗannan sune aukuwan sama da duniya

"Wannan shi ne tarihin sama da duniya" ko "Wannan shi ne labari game da sama da duniya." Mai yiwuwa ana nufi 1) wannan taƙaitaciyar labari ne da aka bayar a Farawa 1:1-2:3 ko 2) Na gabatar da abin da ke faruwa a Farawa 2. in mai yiwuwa ne, juya a hanyar da mutane za su fahimce dukka.

ya halicce su

"Allah Yahweh ya halicce su." A sura 1 marubucin na ambatar Allah da sunar sa "Allah", amma a sura 2 yana kiran shi "Allah Yahweh."

a ranar da Allah Yahweh ya yi

"a sa'ad da Allah Yahweh ya halicci." Kalmar "rana" na nufin iyakar lokacin halitta, ba wani kwana ɗaya ba.

Yahweh

Wannan shi ne sunar da Allah ya bayyanar wa mutanen sa a cikin Tsohon Alkawari. Duba translationWord domin sanin yadda aka juya kalmar Yahweh.

ba tsire-tsiren a duniya

ba tsire-tsiren da ke girma a jeji domin dabbbobi su ci

Ba shuka a filin duniya

ba shuka masu ganyayyeki kamar kayan lambu da mutane da dabbobi za su iya ci

a nome

a yi duk abin da ake bukatan yi domin shuka ta yi girma da kyau

kãsashi

Mai yiwuwa ana nufi 1) wani abu kamar hazo, ko 2) bubbugowar ruwa daga rafi.

fuskar ƙasa dukka

duniya dukka