ha_tn/gen/01/24.md

1.1 KiB

Bari ƙasa ta fid da masu rai

"Bari ƙasa ta fid da abubuwa masu rai" ko "Bari dabbobi dayawa masu rai su rayu a duniya." Wannan umurni ne. Ta wurin umurtar duiya ta fid da masu rai, Allah ya sa duniya ta fid da masu rai. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-imperative)

kowane da irin ta

"domin kowani dabba ta haifar da irin ta"

dabbobin gida, abubuwa masu rarrafe, da dabbobin duniya

Wannan na nuna cewa Allah ya halicci dukka irin dabbobi. Idan harshe ku na da yadda kuke kiran tarin dabbobi, kuna iya amfani da shi, ko kuma kuna iya amfani da wannan.

dabbobin gida

"dabbobin da mutane ke kiwo"

abubuwa masu rarrafe

"ƙananan dabbobi"

dabbobin duniya

"dabbobin jeji" ko "dabbobi masu haɗari"

haka ya kasance

"Ya faru kamar yadda ya ke" ko "haka abin ya faru."Abin da Allah ya umurta ya faru, haka kuwa ya faru.Wannan maganar ya kasance a wurare dayawa a wannan surar kuma yana da ma'ana ɗaya ne a duk inda ya kasance.

Allah ya halicci dabbobin

"Ta haka ne Allah ya halicci dabbobin"

Ya ga cewa yana da kyau

"yana" anan na nufi abubuwa masu rai a duniya.