ha_tn/gen/01/14.md

1.7 KiB

Bari haskoki su kasance a cikin sarari

Wannan umurni ne. Ta wurin umurtar haskoki su kasance, Allah kuwa ya sa sun kasance. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-imperative)

haskoki a cikin sarari

"abubuwan da suke haskakawa a cikin sarari" ko "abubuwan da suke kawo haske a cikin sarari." Wannan na nufin rana, wata, da ta taurari.

cikin sarari

"cikin sararin sama" ko "a babban sararin sama"

raba tsakanin yini da dare

"su raba yini da dare." Wannan na nufin "su taimake mu bambanta tsakanin yini da dare." Rana na nuna yini, wata da taurari kuwa na nuna dare.

su zama alamu

Wannan umurni ne. Ta wurin umurtar cewa su zama alamu, Allah kuwa ya sa sun zama alamu. AT: "Bari su kasance alamu" ko "su kuma nuna" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-imperative)

alamu

Wannan na nufin wani abu ne da ke bayyanar da wani abu.

yanayi na shekara

"yanayin shekara" na nufin lokaci da aka keɓe domin bukukuwa da wasu abubuwan da mutane ke yi.

na yanayin shekara, na kwanaki da shekaru

Rana, wata, da taurari na nuna yadda lokaci ke wucewa. Wannan na bamu damar sani aukuwar kowani mako, watani, ko shekara.

Bari su kasance haskoki a sarari, su kuma haskaka duniya

Wannan umurni ne. Ta wurin umurta cewa su haskaka duniya, Allah kuwa sa sun haskaka duniya. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-imperative)

so haskaka duniya

"su kawo haske a duniya" ko "su sa haske a duniya." Duniya ba ta hasken kanta amma ana haskakata ne, sai ta kuma maimaita hasken.

Haka ya kasance

"Haka ya faru" ko "abin da ya faru kenan." Abin da Allah ya umurta ya faru kamar yadda ya ce.Wannan maganar ya kasance a wurare dayawa a wannan surar kuma yana da ma'ana ɗaya ne a duk inda ya kasance. Dubi yadda aka juya wannan a Farawa 1:6.