ha_tn/gen/01/11.md

1.6 KiB

Bari ƙasa ta fid da tsire-tsire

Wannan umurni ne. Ta wurin ba da umurnin cewa tsire-tsire so fito daga ƙasa, Allah ya sa hakan ya faru. AT: "Bari tsire-tsire su fito daga ƙasa" ko "Bari tsire-tsire su girma daga ƙasa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-imperative)

tsire-tsire: shuka masu ba da tsaba, da itatuwa masu ba da 'ya'ya

"tsire-tsire, kowani shuka mai ba da tsaba da kowani itace mai ba da 'ya'ya" ko "tsire-tsire. Su zama shuka masu tsaba, da kuma itatuwa masu ba da 'ya'ya." An yi amfani da kalmar "tsire-tsire" a nufin kowani shuka da itatuwa.

shuka

Waɗannan 'yan tsire-tsire ne ba kamar manyan itatuwa ba.

itatuwa masu ba da 'ya'ya masu ƙwaya a cikinsu

"itatuwa masu ba da 'ya'ya da ke da ƙwaya a cikinsu"

kowanne bisa ga nasa iri

Ƙwayar za su haifar da itatuwa irin wadda suka fito. ta wurin haka kuwa itatuwa za su "haifar da kansu" (UDB).

Haka ya kasance

"Haka ya faru" ko "abin da ya faru kenan." Abin da Allah ya umurta ya faru kamar yadda ya ce.Wannan maganar ya kasance a wurare dayawa a wannan surar kuma yana da ma'ana ɗaya ne a duk inda ya kasance.

Allah ya ga haka na da kyau

Anan "na" na nufin tsire-tsiren, shuka, da itatuwa. dubi yadda aka juya wannan a cikin Farawa 1:9.

maraice da safiya

Wannan na nufin rana ɗaya ne. Marubucin na magana game da rana ɗaya kamar ranar na rabe a sashi. Rana a al'adar Yahudawa na farawa a fadiwan rana ne. dubi yadda aka juya wannan a cikin Farawa 1:3. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-merism)

kwana na uku

Wannan na nufin kwana na uku kenan da kasancewar duniya. duba yadda ka juya "kwana na farko" a Farawa 1:3 sai a yanke shawara ko za a juya wannan ta hanyar.