ha_tn/gen/01/09.md

1.2 KiB

Bari ruwayen ... su tattaru

Ana iya fassara wannan tare da aikatau. Wannan umurni ne. Ta wurin umurtar ruwaye su tattaru, Allah ya sa sun tattaru. AT: "Bari ruwayen ... tattaru" ko "Bari ruwaye ... zo wuri ɗaya" (UDB) (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-imperative]])

bari sandararriyar ƙasa ya kasance

Ruwan ya rufe ƙasa. Ruwan zai tattaru a gefe, sa'anan ƙasa ya kasance. Wannan umurni ne. Ta wurin umurta sandararriyar ƙasa ya kasance, Allah ya sa shi ya kasance. AT: "Bari a ga sandararriyar ƙasa" ko "bari sandararriyar ƙasa ya kasance a fili" ko "bari ƙasar ya zama a fili" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-imperative)

sandararriyar ƙasa

Wannan na nufin ƙasa ne da ruwa baya rufe ba. Ba ana nufin cewa ƙasar ta bushe da ba za a iya noman ta ba.

Haka ya kasance

"Haka ya faru" ko "abin da ya faru kenan." Abin da Allah ya umurta ya faru kamar yadda ya ce.Wannan maganar ya kasance a wurare dayawa a wannan surar kuma yana da ma'ana ɗaya ne a duk inda ya kasance.

duniya

"ƙasa" ko " filin ƙasa"

Ya ga cewa yana da kyau

"Yana" anan na nufin ƙasar da teku. dubi yadda aka juya wannan cikin Farawa 1:3.