ha_tn/gen/01/06.md

1.3 KiB

Bari a sami fili tsakanin ruwaye, sai ya rarraba tsakanin ruwaye

Waɗannan umurnai ne. Ta wurin umurtar cewa sarari ya kasance, ya kuma raba tsakanin ruwaye, Allah ya sa haka ya faru ya kuwa raba ruwayen. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-imperative)

fili tsakanin

"babban fili tsakanin." Yahudawa sun gane sarari a matsayin wani abu ne mai siffer zobe ko cikin kwano da aka juya kasa.

tsakanin ruwayen

"cikin ruwan"

Allah ya halici sararin sa'an nan ya raba ruwayen

"Ta wannan hanyar ne Allah ya halici sararin da ya kuma raba ruwayen." Sa'ad da Allah yayi magana, abin da ya fada ya faru. Wannan jimlar na bayana abin da Allah ya yi a sa'ad da yayi magana.

haka ya kasance

"Ya faru kamar yadda ya ke" ko "haka abin ya faru." Abin da Allah ya umurta ya faru, haka kuwa ya faru.Wannan maganar ya kasance a wurare dayawa a wannan surar kuma yana da ma'ana ɗaya ne a duk inda ya kasance.

maraice da safiya

Wannan na nufin rana ɗaya. Marubucin na magana game da rana ɗaya kamar ranar na rabe a sashi. Rana a al'adar Yahudawa na farawa a fadiwan rana ne. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-merism)

kwana na biyu

Wannan na nufin kwana na biyu kenan da kasancewar duniya. Duba yadda ka juya "kwana na farko" a Farawa 1:3 sai a yanke shawara ko za a juya wannan ta hanyar.