ha_tn/gen/01/03.md

803 B

Bari haske ya kasance

Wannan umurni ne. Ta wurin umurnin cewa haske ya kasance, Allah kuwa ya sa hasken ya kasance. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-imperative)

Allah ya ga hasken yana da kyau

"Allah ya dubi hasken kuma ya faranta masa." "Kyau" anan na nufin "farantawa" ko "dacewa."

raba tsakanin hasken da duhu

"raba haksen da duhu" ko "mayar da shi haske a wani loto, duhu kuma a wani lokaci." Wannan na nufin halitar Allah na yini da dare .

Wannan shi ne safiya da dare, a rana ta ɗaya

Allah ya yi waɗannan abubuwa a kwanan farko da duniya ya kasance.

maraice da safiya

Wannan na nufin rana ɗaya. Marubucin na magana game da rana ɗaya kamar ranar na rabe a sashi. Rana a al'adar Yahudawa na farawa a fadiwan rana ne. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-merism)