ha_tn/gal/04/06.md

1.3 KiB

ku 'ya'ya ne ... kai ba bawa ne kuma ba, amma ɗa

Bulus ya yi amfani da kalmar yaro namiji anan domin zancen game da gado ne. A al'adan shi da masu karatun shi, an saba ba gado ga 'ya'ya maza, ko da yake ba ko yaushe ba. ba wai yana tanatance ko kuma ware 'ya'ya mata ba ne anan.

Allah ya aiko da Ruhun ɗan sa a cikin zukatanmu, wanda yake kira, "Abba, Uba."

Ta kiran "Abba, Uba" Ruhun na tabbatar da mu 'ya'ya Allah ne kuma yana kaunar mu.

aiko da Ruhun Ɗan sa a cikin zukatanmu

zuciya anan a nufin bangare a mutum da ke tunani ko ji. AT: "aika Ruhun Ɗan sa ya nuna mana yadda za mu yi tunani da zama" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Ɗan sa

Wannan muhimmin lakabi ne na Yesu, Ɗan Allah. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/guidelines-sonofgodprinciples)

wanda ke kira

Ruhu shi ne wanda ke kira.

Abba, Uba

Ta wannan hanya ne yaro ke martaba mahaifinsa a harshen gidan Bulus, amma ba a harshen Galatiyawa masu karatu ba. domin ci gaban harshen waje, fassara wannan kalman "Abba" kamar yadda harsha ku ke yi.

kai ba bawa ne kuma ba ...kai ma magaji ne

Bulus na magana da masu karatun sa kamar mutum daya ne. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-you)

magaji

ana magana game da mutanen da Allah yayi wa alkawarai kamar za su gaji wani dukiya ne da ga wani ɗan iyali. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)