ha_tn/ezk/01/24.md

728 B

Muhimmin Bayani:

Ezekiyel ya ci gaba da faɗi game da wahayinsa game da rayayyun halittu.

Kamar ƙarar ruwaye masu yawa

Wannan kawai yana nufin "ruwa mai yawa." Zai iya nufin babban kogi ko babban ambaliyar ruwa ko raƙuman ruwa da ke buguwa a teku. Duk waɗannan suna da ƙarfi sosai.

Kamar muryar Mai Iko Dukka

Littafi Mai Tsarki wani lokaci yakan kira tsawa “muryar Maɗaukaki”. AT: "Ya yi kama da muryar Allah Maɗaukaki" ko "Ya yi kama da tsawar Mai Iko Dukka" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Sai murya ta zo daga saman sararin

"Wani wanda yake saman sararin yayi magana." Idan kuna buƙatar faɗin muryar waye wannan, mai yiwuwa ya kamata ku gane ta muryar Yahweh ce (Ezekiyel 1: 3).