ha_tn/ezk/01/04.md

1005 B

Mahadin Zance:

Ezekiel ya ci gaba da kwatanta wahayinsa.

babban girgije mai wuta na haskakawa kewaye da shi

Ana iya fassara wannan azaman sabon jumla: "Guguwar tana da gajimare mai girma da wuta tana walƙiya a ciki"

Daga cikin tsakiyarsa siffar waɗansu masu rai huɗu

Anan sunan mara bayyanan "kamance" yana nufin cewa abin da Ezekiel ya gani yayi kama da waɗannan abubuwa. Ana iya fassara kalmar da kalmar magana. AT: "abin da yayi kama da rayayyun halittu guda huɗu" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-abstractnouns)

suna da kamannin mutum

Cikakken sunan "bayyanuwa" za a iya fassara shi azaman kalmar magana. AT: "halittun nan huɗu sun yi kama da mutane" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-abstractnouns)

amma kowannensu yana da fuskoki huɗu, kowacce halittar kuma nada fikafikai huɗu

"amma kowanne daga cikinsu yana da fuskoki daban-daban da fikafikansa guda hudu." Kowane taliki yana da fuska a gaba, yana da fuska a bayansa, yana da fuska a kowane gefen kansa.