ha_tn/exo/32/12.md

1.0 KiB

Muhimmin Bayani:

Musa ya cigabda wa Allah magana kada yă hallaka Isra'ila.

Me ya sa za ka sa Masarawa su ce, 'Ya sa su sun fito da mugun nufi, don yă kashe su cikin duwatsu ya kuma shafe su daga fuskar duniya?'

Musa ya yi amfani ne da wannan tambayar domin ya lallashe Yahweh kada ya yi fushi da mutanensa. Ana iya juya wannan tambayan gangancin zuwa magana. AT: "Idan ka hallaka mutanenka, ai Masarawa suna iya ce, 'Ya sa sun fito ...don yă shafe su daga fuskar duniya' (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

fuskar duniya

"daga duniya"

ka janye daga zafin fushinka

"kada daina fushi haka"

zafin fushinka

Musa yana maganar fushin Allah kamar wani wuta ne mai ƙuna. AT: "mummunan fushinka" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Ka tuna da Ibrahim

"Ka yi tunanin Ibrahim"

rantse

"yi alkawali" ko kuma "ka ɗauki alkawari"

Za su gaje ta har abada

Wato za su mallaki kasar kenan. AT: "Za su mallaki kasar har'abada" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)