ha_tn/exo/16/06.md

1.3 KiB

Su wanene mu da zau ki yi gunaguni gãba da mu?"

Musa da Haruna sun yi amfani ne da wannan tambayan domin su nuna wa mutanen cewa wauta ne su yi gunaguni gãba da su. AT: "Ai ba mu da cikakken iko da har za ku yi gãba da mu." ko kuma "Ai wauta ne ku yi gunaguni gãba da mu, domin ba mu iya yin abinda kuke so ba." (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-rquestion]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-explicit]])

gurasa

Musa yana maganar abincin da zai turo daga sama kamar gurasa ne abincin. Isra'ilawan za su ci wannan abinci a kowace rana ne, kamar yadda suke cin gurasa kullum kamun wannan tanaɗi. Duba yadda kuka juya wannan a 16:4. AT: "abinci" ko kuma "abinci kamar gurasa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Su wanene Haruna da ni?

Musa yana amfani ne da wannan tambayan domin yă nuna wa mutanen cewa shi kansa da Haruna basu da iko su basu abinda suke so. AT: "Haruna dai da ni ba za mu iya baku iyakar abinda kuke so ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

Gunagunanku ba gãba da mu bane; gãba ne da Yahweh

Mutanen suna gunaguni gãba da Musa da Haruna, wadda bayin Yahweh ne su. Don haka, ta wurin yin gãba da su, mutanen suna gunaguni gãba ne da Yahweh ainun. AT: "Gunagunanku ba ma gãba da mu bane; gãba ne dai da Yahweh, domin mu dai bayinsa ne" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)