ha_tn/exo/15/06.md

1.8 KiB

Hannunka na dama, Yahweh, ɗaukakakke ne cikin iko

Musa yana maganar Allah kamar Allah yana da hannu ne. Hannun damar Allah na nufin Ikon Allah ko kuma abubuwad da Allah ke yi da iko. AT: "Yahweh, ikon ka ɗaukakakke ne" ko kuma "Yahweh, abin da ka yi ɗaukakakke ne cikin ikon" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

hannunka na dama, Yahweh, ya rugurguza maƙiyi

Musa yana maganar Allah kamar Allah yana da hannu ne. Hannun damar Allah na nufin ikon Allah. AT: "Yahweh, ikon ka ya rugurguza makiyi" ko kuma "Yahweh, ta wurin ikon ka, ka rugurguza makiyi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

ya rugurguza maƙiya

Musa yana maganar maƙiyi kamar wani abu ne mai saukin fashewa da zai iya rugurguzawa kamar gilashi ko tukwance. AT: "ya hallaka maƙiyi gabaɗaya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

waɗanda suka taso gãba da kai

Ana maganar tawaye da Allah ne kamar tayarwa ne da shi. AT: "waɗanda suka tayar maka" maƙiyanka" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

ka aika da hasalarka

Musa yana maganar hasalar kamar wani bare ne da Allah ya aika ya yi wani abu. AT: "ka nuna hasalarka" ko kuma " ka yi bisa hasalarka" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-personification)

ya cinye kamar ciyawa

Musa yana maganar hasalar Allah ne kamar wuta ne da ke iya cinye abubuwa gabaɗaya. Maƙiyin sun hallalaka kamar ciyawa da a wuta. AT: "ya hallaka maƙiyanka ne kamar wuta ne da ke ƙona ƙara" (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-metaphor]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-simile]])

da hucin nunfashin hancinka

Musa yana maganar Allah ne kamar Allah yana da hanci, kuma kamar yana maganar nunfashi ne kamar Allah ya hura nunfashi ne daga hancinsa. AT: "ku hura bisa tekun da" (UDB). (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-personification)