ha_tn/est/09/23.md

856 B

Muhimmin Bayani:

Wannan wuri ya kammala yawacin labarin Esta domin a bayyana dalilin yin bikin Furim.

Haman ɗan Hamedata Ba'agage

Wannan suna ne da kwatancen Haman, ɗaya daga cikin shugabannin sarki. A duba yadda aka fassara wannan a cikin Esta 3:1. (Duba: rc://*/ta/man/translate/translate-names)

ya kuma jefa Fur (wato, ya jefa ƙuri'u)

"Fur" kalmar Fasiya ne na "ƙuri'u." Kalmar "ya jefa ƙuri'u" ya bayyana ma'anar "ya jefa Fur."

Amma da zancen ya kai ga sarki,

Za a iya fassara juyin Ibraniyawa ya kasance da ma'anar, "Amma da Esta ta zo gaban sarki." Wasu juyin zamani sun ɗauki wannan fassarar.

makircin da Haman ya ƙulla gãba da Yahudawa shi koma kansa

"shi koma kansa" na ma'anar a yiwa Haman haka. AT: "makircin da Haman ya ƙulla gãba da Yahudawa bari a yi ma shi" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)