ha_tn/est/09/01.md

1.8 KiB

watan sha biyu, wanda shi ne watan Ada, a ranar sha uku

A duba yadda aka fassara irin wannan zance a cikin Esta 3:13.

lokacin da za a aiwatar da shari'a da kuma dokar sarki

A nan "aiwatarwa" kari ne da ke ma'anar yin wani abin da aka umarta ko shirya. Za a iya faɗin wannan a matsayin aikatau. AT: "lokacin da mutanen su ke gab da aiwatar da shari'a da kuma dokar sarki" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-idiom]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-activepassive]])

zasu sha karfinsu

Shan ƙarfin mutane kari ne da ke ma'anar kayar da su. AT: "su kayar da Yahudawa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

aka juyad

"aka juyad da al'amarin." Juyad da al'amarin misali ne da ke ma'anar akasin abin da aka zaci zai faru. AT: "akasin ne ya faru" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

lardunan

A duba yadda aka fassara wannan a cikin Esta 1:1.

su tayar wa waɗanda suka so su kawo masu bala'i

Tayar wa mutane zance ne da ke nufin yin yaƙi gãba da su. AT: "su yi yaƙi da maƙiyansu" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

waɗanda suka so su kawo masu bala'i

Kawo bala'i ga mutane kari ne da ke ma'anar haddasa bala'i ya faru da su. A wannan yanayin yana nufin hallakar da su. AT: "waɗanda suka nemi su hallakar da su" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

Babu wanda ya iya tsayayya dasu

Tsayayya da mutane na nufin hana harinsu. AT: "Ba bu wanda ya iya hana kai harin Yahudawa" ko "Ba bu wanda ya iya yin nasara a yaƙi gãba da Yahudawa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

gama tsoronsu ya abko wa dukkan mutanen

Tsoron mutane ya abko masu na nufin mutane na zama cikin tsoro ƙwarai. AT: "dukkan mutanen suka zama cikin tsoron Yahudawa ƙwarai" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)