ha_tn/est/07/08.md

1.2 KiB

ɗakin da aka shayar da su ruwan inabi

Za a iya faɗin wannan a matsayin aikatau. AT: "inda barorin suka shayar da su ruwan inabi" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

kujera

dogon wurin zama inda wani zai iya zaunawa ko ya kwanta

Zai ci mutuncin sarauniya a gabana a cikin gidana?

Sarki yayi wannan tambaya ne domin ya nuna mamakinsa da haushin abin da Haman ya ke yi. Za a iya fassara wannan a matsayin jimla. AT: "Har ma yana neman ya kai wa sarauniya hari a gabana a cikin gidana!" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

ci mutuncin sarauniya

"kai hari ga sarauniya." Wannan wata hanyar sauƙi ce ta faɗin fyaɗe. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-euphemism)

Da zarar fitar wannan magana daga bakin sarki

Fitowar zance daga baki misali ne da ke nufin yin magana. AT: "da zarar sarki ya ce haka" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

barorin suka lulluɓe fuskar Haman

Lallai sun yi haka ne saboda sun fahimci sarki yana so a kashe Haman. AT: "barorin sun lulluɓe fuskar Haman ne alamar cewa za a kashe shi" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-explicit]] da [[rc:///ta/man/translate/translate-symaction]])