ha_tn/deu/30/01.md

1.5 KiB

Muhimmin Bayani:

Musa ya yi magana da Isra'ilawan kamar su mutum ɗaya ne. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-you)

Sa'ad da dukkan waɗannan abubuwa suka zo kanku

A nan "waɗannan abubuwan" na nufin albarku da la'anannu da an bayana a sura 28-29. Jimlar "sun zo kanku" ƙarin magana ne da ke nufin faru. AT: "Sa'ad da dukkan waɗannan abubuwan sun faru da ku" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

dana shirya a gabanku

Wannan na maganar albarku da la'anu da Musa ya gaya wa mutanen kamar abubuwa ne da ya shirya a gabansu. AT: "da yanzu na rigaya na faɗa maku" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

tuna da su

Wannan ƙarin magana ne. AT: "tuna da su" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

cikin dukkan sauran al'ummai

"sa'ad da ku na zama a cikin sauran al'imman"

kora ku

"ya tilasta ku ku tafi"

yi biyayya da muryarsa

A nan "murya" na nufin abin da Yahweh ya faɗa. AT: "yi biyayya da abin da ya faɗa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

da dukkan zuciyarku da kuma dukkan ranku

Karin maganar "da dukkan ... zuciya" na nufin "gabadaya" da "da dukkan ... rai" na nufin "da dukkan kasancewarku." AT: "da dukkan kasancewarku" ko "da dukkan ƙarfinku." Fasara wanan kamar yadda yake a 4:29. (Dubi: [[rc:///ta/man/translate/figs-idiom]] and [[rc:///ta/man/translate/figs-doublet]])

komo da ku daga bauta

"sake ku daga bauta." AT: "sake ku daga wanda sun kama ku" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-abstractnouns)