ha_tn/deu/28/13.md

1.0 KiB

Muhimmin Bayani:

Musa ya cigaba da magana da Isra'ilawan kaman su mutum ɗaya ne. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-you)

kan, ba wutsiya ba

Wannan maganan ya nuna al'umman Isra'ila kaman dabba kuma na nufin cewa Isra'ilawan za su zama shugabane akan wasu al'ummai, ba kuwa bayi ba. Isra'ilan za su fi da iko, kuɗi da daraja. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

a ku kasance kullum a bisa ... ba a ƙasa ba

Isra'ilawan za su yi shugabanci akan wasu amma ba za su samu wasun da za su shugabance su ba.

Ina umarce ku

Musa na magana da dukka Isra'ilawan. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-you)

idan ba ku juya daga waɗannan maganganu da nake umartanku a yau, ga hannun dama ko hagu ba, har ku bi waɗansu alloli ku bauta masu

An yi maganar rashin biyayya wa Yahweh da kuma bautan wasu alloli kamar mutum ya juya ya kuma kwace daga kalmomin Yahweh. AT: "idan ba ku yi rashin biyayya da abin da ina umartanku yau ta wurin bautan wasu alloli ba"(Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)