ha_tn/deu/24/01.md

725 B

Muhimmin Bayani:

Musa ya cigaba da magana da mutanin Isra'ila.

Sa'adda namiji ya ɗauki mata ya aure ta

Wannan maganar "ɗauki mata" da "aure ta" na nufin abu ɗaya. AT: "Sa'dda namiji ya auri mace" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-doublet)

idan bata sami tagomashi a idanunsa ba

A nan "a idanunsa" na nufin dukkan mutumin. AT: "idan ya yanke shawarar cewa ba ya son ta kuma" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)

saboda ya sami wani abin aibatarwa da ita

"saboda wasu dalilai, ya yanke shawarar cewa ba ya so ya rike ta"

dole ya rubuta mata takardar saki

"dole ya ba matarsa takardar cewa ba su tare kuma"

zata iya tafiya ta zama matar wani

"zata iya tafiya ta aure wani mutum"