ha_tn/dan/11/25.md

2.3 KiB

Muhimmin Bayani:

Bayani na gabaɗaya: Mala'ikan ya cigaba da magana ga Daniyel

Zai ta da ikonsa da zuciyarsa

Ikonsa da zuciyarsa (wato, gabagaɗi) an ambace su ne kamar su mutane ne da wani zai iya tashe su don su yi wani abu.AT:"zai maishe da kansa da iko zai kuma zama da gabagaɗi" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-personification)

zuciya

Wannan na nufin gabagaɗi. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

da babbar rundunar yaƙi

"da babbar rundunar yaƙi da zai shirya"

zai ja dagar yaƙi

"zai yaƙe shi"

ba zai iya tsayawa

ba zai iya tsayawa na nufin an ci nasara akan sa.AT:"za'a yi nasara akan sarkin kudu" ko "za'a yi nasara akan dakarunsa" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

waɗanda suka ci abin sa

A nan ana maganar masu bashi shawara. Abin da aka saba yi ne amintaccen mai ba sarki shawara ya ci abinci tare da shi. AT:"masu bada shawarar da sarki ya aminta da su" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Rundunarsa za'a share su kamar ambaliya

A nan an yi magana kan matsananciyar nasara akan wasu dakarai kamar yadda ambaliya ke share duk abin da tayi karo da shi.AT:"abokin gabar zai yi nasara da dakarunsa" ko "abokin gabar sa zai yi nasarar lalata dakarunsa kamar yada ambaliya ke tafiya da duk abin da ta haɗu da shi a hanyar ta" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

da yawan su zasu faɗi kisassu

A nan "faduwa" habaici ce da ke nufin mutuwa a baƙin daga, saboda haka "faduwa" da "mutuwa" na da ma'ana kusan ɗaya. AT:"dakarunsa da yawa zasu mutu a filin daga" (Duba: [[rc:///ta/man/translate/figs-idiom]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-doublet]])

da zuciya mai mugun fatã ga juna

A nan "zuciya" na nufin ƙudirin mutum. An yi maganar kudiri a nan kamar wani abu da wani zai ajiye a wani wuri. AT:"kowa na shirin mugunta ga ɗayan" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

za su zauna a teburi ɗaya

zama a teburi ɗaya na nufin magana da juna. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

amma ba za ta zama da amfani ba

"amma maganganun su bazasu taimake su ba"

Gama matuƙa za ta zo a ƙayadadden lokaci

Wannan ya bayyana dalilin da yasa zaman su ba zai yi nasara. AT:"sakamakon ayyukan su zai zo ne kawai a lokacin da Allah ya shirya" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)