ha_tn/dan/07/15.md

765 B

ruhuna ya damu a cikina...wahayoyin da na gani kuwa a cikin raina suka dame ni

Jimloli biyun nan sun nuna yadda Daniel ke ji. Na biyun yafi bada cikakken bayani game da na farkon, yana bayyana ɗacin zuciyarsa. (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-parallelism)

ruhuna ya kaɗu

A nan "ruhuna" na nufin Daniyel da kansa. AT:"na damu sosai a cikin raina" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)

daga cikin waɗanda ke tsaye a wurin

Wannan ɗaya daga cikin talikan da ke tsaye a gaban kursiyin Allah (UDB). Ma'anonin kan zama 1) Wadannan mala'iku ne, ruhohin da ke bautawa Allah 2) wadannan mutanene wanda suka mutu yanzu suke cikin sama.

ya nuna mini

"ya sheda mini" (UDB) ko "ya bayyana mini"

wadannan abubuwa

"abubuwan da na gani"