ha_tn/dan/07/09.md

1.8 KiB

Muhimmin Bayani:

Yawancin abin da ke aya 9-14 yare ne mai hannun riga amma ma'anar su ɗaya. Saboda wannan dalili ne, Littafi Mai Tsarki juyin ULB da UDB suka yi su da tsarin waƙa. (Duba: [[rc:///ta/man/translate/writing-symlanguage]] da [[rc:///ta/man/translate/figs-parallelism]])

an shirya kursiyoyi

Za'a iya bayyana wannan da gabagaɗi. AT:"wani ya shirya kursiyoyi a wuri ɗaya" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

Mai dogon zamani

Wannan sunan na Allah da ke ma'anar yana rayuwa dukan zamanai. AT:" Wanda ke rayuwa har abada" ko "wanda ke rayuwa koyaushe"

ya dauki kursiyi ... Suturarsa ... gashin kansa

Wurin ya bayyana Allah kamar wanda ya zauna, da sutura da suma kamar mutum. Wannan ba yana nufin Allah kamar mu yake, amma yadda Daniyel ya ga Allah a wahayin ne.

ya dauki wurin zaman sa

Wannan habaici ne da ke nufin ya zauna. AT:" ya zauna a kan kursiya" (Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)

Tufafin sa fari fat kamar dusar ƙanƙara

An kwatanta tufar sa da dusar kankara don a nuna fara ce sosai. AT:"tufafin sa fari fat ne"

gashin kansa kuwa kamar farin ulu

An kwatanta sumar Allah kamar farin ulu. Ma'anonin zasu iya zama 1) tana da fari ƙwarai (UDB) ko 2) tana da kauri da kyau. Duba: rc://*/ta/man/translate/figs-simile)

farin ulu

"tsabtataccen ulu" ko ulun da aka wanke"

Kursiyinsa harsunan wuta ne... gargarensu kuwa suna ci da wuta

wannan na nuna kursiyin Allah da gargaren sa kamar an yi su da wuta. Kalmar"wuta" da "wuta maici" na ma'anar kusan abu ɗaya za kuma a iya fasara su ta hanya ɗaya.

gargaren ta

Ba a fayyace dalilin da yasa aka danganta mulkin Allah da cewa yana da gargare. A zahiri kursiyi bashi da gargare, amma nassin ya nuna a fili cewa wannan kursiyin yana da wadansu gargare. A yi amfani da wata kalma domin "gargare" idan zai yiwu.