ha_tn/col/04/02.md

836 B

Muhimmin Bayani:

Kalmar "mu" a nan na nufin Bulus da Timoti ba 'yan Kolosi ba. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-exclusive)

Ku cigaba da himmantuwa ga yin addu'a

"ku dinga yin addu'a da aminci" ko kuma "ku dinga yin addu'a ba fasawa"

Allah ya buɗe kofa

Buɗe kofa a nan na nufin ba wa mutum zarafi ya yi wani abu. AT: "Allah zai tanadar da zarafi" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

asarin gaskiyar Almasihu

Wannan yana nufin bisharar Yesu Almasihu, wanda ba a gane ba kafin Yesu ya zo.

Don wannan ne nake cikin sarƙa

"sarƙa" a nan na nufin kasancewa a cikin kurkuku. AT: "Saboda shelar sakon Yesu Almasihu ne yanzu ina cikin kurkuku" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

Ku yi addu'a domin in iya faɗinsa daidai

"Ku yi addu'a in iya faɗin sakon Yesu Almasihu daidai"