ha_tn/col/03/12.md

1.0 KiB

A matsayin ku na zaɓaɓɓun Allah, masu tsarki da ƙaunatattu

AT: "A matsayin waɗanda Allah ya zaɓa wa kansa, wadda yake marmarin ganin cewa suna rayuwa dominsa kaɗai, kuma wadda yake ƙauna" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

sai ku yafa jinƙai, ayyukan kirki, sauƙin kai, kamewa da haƙuri

Aan maganar waɗannan halaye kamar wasu tufafi ne da ake iya sa wa. AT: "ku zama da jinƙai, halin kirki, sauƙin kai, kamewa, da zuciyar haƙuri" ko kuma "ku zama masu jinƙai, halin kirki, sauƙin kai, kamewa, da hakuri" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

Yi haƙuri da juna

"Ku yi haƙuri da juna" ko kuma "Ku riƙe juna ko da kun ba wa juna kunya"

Ku yi wa juna alheri

"ku bi da juna fiye da yanda sun cancanci ku bi da su"

na da damuwa da

AT: "na da wani dalilin da" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-abstractnouns)

ku kasance da ƙauna, wanda ita ce cikakkiyar kammala

AT: "ku yi ƙaunar juna domin hakan zai haɗa ku tare" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)