ha_tn/act/25/17.md

1.1 KiB

Saboda haka

"Da shike abinda na faɗa maku gaskiya ne." Festas ya fito ce gaya masu cewa duk mutumin da aka kai ƙaransa zai bayyana a gaban masu ƙaran don ya yi nasa magana akan ƙaran.

da duk suka taru ana

"da shugabannin Yahudawan sun zo sun same ni anan"

na zauna a kujerar shari'a

A nan "kujerar sheri'a" na nufin shari'ar da Festas yake kan yi akan Bulus. AT: "na zauna a bisa kujerar in yanke shari'a" ko kuma "na zauna a matasyin alkali" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

na ba da umarni a kawo mutumin

AT: "na umarci sojojin su kawo Bulus gabana" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

addininsu

A nan "addini" na nufin ra'ayin mutane akan rayuwa da kuma abinda ya wuci ikon ɗan Adam.

a shari'anta shi kan waɗannan ƙararraki

A "shar'anta" karin magana ne da ke nufin a yanke wa mutum hukunci don a san ko mutumin yana da laifi ko babu. AT: "ya je yi masa shari'a a akan waɗannan laifuffuka" ko kuma "don mai yanke shari'a yă san ko waɗannan ƙararraki a kansa gaskiya ne ko ba gaskiya ba ne" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-idiom)