ha_tn/act/25/11.md

959 B

Idan lallai na yi laifi ... kada kowa ya bashe ni gare su

Bulus yana magana ne idan maganar da za a kawo a kansa gaskiya ne. Idan yana da laifi, zai karɓi hukuncin, amma shi ya tabbatar cewa ba shi da laifi. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-hypo)

idan na yi abin da ya cancanci mutuwa

"idan na aikata laifin da ya cancanci mutuwa ne ya zama hukunci na"

idan zarginsu ƙarya ne

"idan ƙararraki da aka yi a kaina ba gaskiya ba ne"

kada kowa ya bashe ni gare su

Wanna na iya nufin 1) Festas bashi da iko bisa ga shari'a ya bashe Bulus ga waɗannan masu zargin ko kuma 2) Bulus yana cewa idan ba shi da laifin komai, kada gwamna ya amince da roƙon Yahudawa.

Ina ɗaukaka ƙarata zuwa ga Kaisar

"Ina roƙo a kai ni gaba Kaisar don ya shar'anta ni"

da majalisa

Ba wannan Majalisar bane ake ta maganar su a matsayin "majalisa" a Ayyukan Manzanni gabaɗaya. Wannan ne majalisar siyasa da ke gwamnatin Roma. AT: "da nasa mashawarta"