ha_tn/act/24/14.md

1.7 KiB

na sanar maka da wannan

"Na shaida maka wannan" ko kuma "Na furta maka wannan"

cewa bisa ga hanyar nan

Jimlar nan "hanyar" wata laƙabi ne da ke nufin masubi a zamanin Bulus.

suke kira ɗariƙa

Wanna wata ƙaramar ƙungiya a cikin manyan ƙungiyoyi. Tartilus yana ganin masubi a matsayin wata ƙaramar ƙungiya a cikin adinin Yahudanci. Duba yadda aka juya "ɗariƙa" a [24:5]

haka ni ma nake bautawa Allah na kakanninmu

Bulus yana amfani ne da wannan kalmar "haka" don yă nuna cewa shi, a matsayinsa na maibin Yesu, yana bauta wa Allah yadda kakkaininsu na Yahudawa suka yi. Yana shugabantar wata "ɗariƙa" ko kuma yana koyar da wata sabuwan abu da ke gãba da addininsu na zamanin dã.

kamar yadda waɗannan mutanen

"kamar yadda waɗannan mutanen suka yi" Anan "waɗannan" na nufin Yahudawa masu zargin Bulus a kotu.

cewa za a yi tashin matattu, masu adalci da miyagu duka

Ana iya sanar da kalmar nan "tashin" zuwa "ta da" AT: "cewa Allah zai ta da dukkan waɗanda suka mutu, da masu adalci da marasa adalci" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-abstractnouns)

masu adalci da miyagu duka

Wannan na nufin mutane masu adalci da mugayen mutane. AT: "mutane masu adalci da mutane marasa adalci" ko kuma "waɗanda suka aikata abinda ke daidai da waɗanda suka aikata abinda ba daidai ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-nominaladj)

kullum nake ƙoƙarin

"nake himma kullum" ko kuma "ina iya ƙoƙari"

zama da lamiri mara abin zargi a gaban Allah

A nan "lamiri" nan nufin tunani ko kuma hankalin mutum da ke iya sanin abinda ke daidai da wanda ba daidai ba. AT: "zama marar laifi" ko kuma "in riƙa aikata abinda ke daidai" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

a gaban Allah

"a gaban Allah"