ha_tn/act/22/14.md

1.2 KiB

nufinsa

"abinda Allah ke shiryawa yana kuma sa yă faru"

ka kuma ji muryar da ke fitowa daga bakinsa

Da "murya" da "baƙi" duka suna nufin mai magana. AT: "ka kuma ji shi yana magana da kai kai tsaye" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)

ga dukkan mutane

A nan "mutane" na nufin jama'a maza da mata. AT: "ga dukkan jama'a" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-gendernotations)

Yanzu

Ana amfani ne da kalmar nan "yanzu" a nan ba wai don yana nufin "a daidai wannan sa'a" ba, amma domin a jawo hankali ne ga wata muhimmin zance da ke bin wannan.

me ka ke jira?

An yi amfani ne da wannan tambaya domin a gargaɗe Bulus ya yi baftisma. AT: "Kada ka jira" ko kuma "Kada ka ɓata lokaci" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

a yi maka baftisma

AT: "bari in yi maka baftisma" ko kuma "karɓi baftisma" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

a wanke zunubanka

Kamar yadda wanke jiki ke cire datti, kira ga sunan Yesu domin gafarrar zunubai yana tsabtacce zukatan mutum daga zunubi. AT: "ka roƙa gafarrar zunubanku" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)

kana kira bisa sunansa

A nan "suna" na nufin Ubangiji. AT: "kana kira bisa Ubangiji ko kuma "kana dogara ga Ubangiji"