ha_tn/act/21/22.md

1.1 KiB

maza huɗu da suka ɗauki wa'adi

"maza huɗu da suka yi wa Allah alkawari." Wato irin alkawarai wanda mutum ba zai sha ruwan inabi ba ko kuma yă aske gashin kansa har sai bayan wasu lokatai da aka keɓe.

Tafi da waɗannan ka tsarkake kanka tare da su

Sai sun tsarkake kansu kamun su iya shiga sujada a haikalli. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

ka ɗauki dukan dawainiyar su

"ka biya masu dukkan buƙatunsu." Kashe kanshen za su tafi dukka wajen siyan ɗan tinkiya na mace da na miji, rago, da kuma hatsida baye bayen sha. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

don su samu su yi aski

Wannan alama ne cewa mutum ya kammala alkawarin da ya yi wa Allah. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-symaction)

abubuwan da ake faɗi a kanka

AT: "abubuwan da mutane ke faɗi a kanka" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

kiyaye shari'a

Ana maganar kiyaye shari'a ne kamar shari'ar shugaba ne da mutane ke iya bi a baya. AT: "yi biyayya da shari'a" ko kuma "yi rayuwa da ta dace da shari'ar Musa da kuma sauran al'adun Yahudawa" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metaphor)