ha_tn/act/13/23.md

1.3 KiB

Daga zuriyar mutumin nan

"Daga Zuriyan Dauda." An saka wannan a farkon jimalan ne domin a nanata cewa lallai ne mai ceton ya zama wani daga zuriyan Dauda. (Dubi: [13:22])

Allah ya fito wa Isra'ila

Wato jama'ar Isra'ila kenan. AT: "ba wa jama'ar Isra'ila" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

kamar yadda aka alkawarta zai yi

"kamar yadda Allah ya alkawarta zai yi"

baftimar tuba

AT: "baftismar yin tuba" ko kuma "baftismar da mutane ke roƙa a masu idan suna so su tuba daga zunubansu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-abstractnouns)

Wanene ni a tsamanin ku?

Yahaya ya yi wannan ta tambayan ne domin ya sa mutane su yi tunanin ko shi wanene. AT: "Yi tunani ko ni wanene" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

Ba nine shi ba

Yahaya yana magana ne game da Almasihu, wadda a ke zaton zuwansa. AT: "Ba nine Almasihu ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

Amma ku saurara

Wannan yana nanata muhimmancin maganar da zai biyo baya.

wani mai zuwa bayana

Wato Almasihu kenan. AT: "Almasihu zai zo ba da jimawa ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

wanda maballin takalminsa ban isa in kwance ba

"Ni ban isa in kwance takalminsa ba." Shi Almasihu ɗin ya fi Yahaya daraja har ma bai ji ya isa ya yi mafi kaskancin abu masa ba.