ha_tn/act/12/18.md

944 B

Sa'anda gari ya waye

"da safe"

ba karamar hargowa ce ta tashi a cikin sojojin ba, game da abin da ya faru da Bitrus

A nan amfani ne da wannan jimlar don a nanata zahirin abinda ya faru. AT: "an samu wata babbar hargowa a cikin sojojin game da abinda ya faru da Bitrus" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-litotes)

Bayan da Hiridus ya neme shi kuma bai same shi ba

"Bayan da Hiridus ya neme Bitrus bai iya samun shi ba"

Bayan da Hiridus ya neme shi

Wannan na iya cewa 1) "da Hiridus ya ji cewa Bitrus ya bata, ya je da kansa ya neme shi a kurkuku" ko kuma 2) "da Hiridus ya ji cewa Bitrus, ya aike sauran sojojin su duba kurkukun."

ya tambayi masu tsaron kuma ya bada umarni a ƙashe su

A mulkin Roma, hukuncin da ake ba wa masu taron kurkuku idan wani daga kurkuku ya gudu shi ne a ƙashe masu gadin gidan kurkukun.

Sai ya gangara

An yi amfani ne da wannan kalmar "ya gangara" domin Kaisariya yana kasa da Yahudiya.