ha_tn/act/12/13.md

1.1 KiB

ya ƙwanƙwasa

"Bitrus ya ƙwanƙwasa." Taɓa ƙofa wata al'ada ne na yau da kullum a Yahudanci da ke sa mutane su san cewa an zo masu fatan ziyara. Kuna iya canza wannan ya yi daidai da al'adan ku.

kofar gidan

"ƙofar shiga gidan" ko kuma "ƙofar shiga daga kan titi zuwa hařabar gidan"

ta zo don ta buɗe ƙofar

Ta zo ƙofar ta tambaya wa ke ƙwanƙwasawa"

don farin ciki

"saboda matuƙar farin ciki" ko kuma "cike da farin ciki"

ta kasa buɗe ƙofar

"bata buɗe kofar ba" ko kuma "ta manta ta buɗe kofar"

ta koma ɗaki a guje

Ka iya so ma ce "wurga da gudu zuwa cikin ɗaki da ke gidan"

ta basu labari

"ta faɗa masu" ko kuma "ta ce"

tsaye a bakin ƙofa

"tsaye a wajen ƙofar." Har yanzu Bitrus na nan tsaye a waje.

Kin haukace

Mutanen ba kadai sun ƙi yarda da ita ba, amma suka tsauta mata cewa tana hauka. AT: "kina hauka"

ta nace da cewa haka ne

"ta nace cewa abinda ta faɗa gaskiya ne"

Suka ce

"suka amsa"

Mala'ikansa ne

"Abinda kin gani, malaikan Bitrus ne." Wasu Yahudwa sun gaskanta da mala'iku masu tsaro, saboda haka me yiwuwa suna ɗaukan cewa mala'ikan Bitrus ne ya zo wurinsu.