ha_tn/act/08/32.md

818 B

kamar ɗan rago a hannun masu sosayarsa bai buɗe baki ba

Masu soyarsa sune masu aske gashin rago domin a iya amfani da shi.

Cikin kaskancinsa aka yi masa shari'a da rashin adalci

AT: "Aka wulakãntashi kuma ba masa shari'a da adalci ba" ko kuma "ya bar masu masa zargin sa suka ci mutuncinsa ya kuma sha wahalan rashin adalci" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)

Wa zai bada tarihin tsararsa?

Ana amfani ne da wannan tambayan domin a nanata cewa babu tsararsa. AT: "Babu wanda zai iya magana akan tsararsa, gama ba za a samu ko ɗaya ba" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

an ɗauke ransa daga duniya

Wannan na nufin mutuwarsa. AT: "Mutane ne suka kashe shi" ko kuma "mutane ne suka ɗauki ransa daga duniya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)