ha_tn/act/08/26.md

1.7 KiB

Yanzu kuwa

Wannan ya sa alamar canjin yanayin labarin ne. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/writing-newevent)

Tashi ka tafi

Waɗannan kalamun aikin na aiki tare ne domin nanata cewa ya shirya ya fara tafiya mai nesa da zai ɗauki ɗan loƙaci. AT: "Shirya don tafiya"

da ta yi ƙasa daga Urushalima zuwa Gaza

An yi amfani ne da wannan jimlar "yi ƙasa" domin Urushalima na sama da Gaza.

wannan hanyar yana cikin hamada

Masu ilimi sun yarda cewa Luka ya ƙara wannan maganar domin ya bayyana yankin da Filibus zai tafi. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/writing-background)

Sai

Kalmar nan "sai" na jan hankalinmu zuwa ga wani sabon mutum da ya shigo labarin. Yana iya yiwuwa harshenku tana da wata hanyar yin haka. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/writing-participants)

bãbã

Nanacin "bãbã" anan na game da matsayin da mutumin Habasha ke da shi a gwamnati, ba kawai domin yanayin sa na fiɗiya ba.

Kandakatu

Wannan wata lakani ne da ake kiran duk sauraniya a Habasha. Yana kamar yadda ake amfani da kalmar Fir'auna wa duk sarki a Masar. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/translate-names)

Ya zo Urushalima domin ya yi ibada

Wannan na nuna cewa shi ba'alummi ne wadda ya gaskata da Allah, ya kuwa zo ya yi wa Allah ibada a haikali. AT: "ya zo ne ya yi wa Allah ibada a haikalin da ke Urushalima" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-explicit)

karussarsa

Mai'yiwuwa "keken doki" za ta fi shiga da wannan yanayin. An fi ambata karusarsa a matsayin abin hawa zuwa yaƙi, ba lallai abin hawa domin tafiya mai nesa ba. Kazalika, mutane na iya tuƙin karusarsa a tsaye.

yana karanta Littafin annabi Ishaya

Wato littafin Ishaya da ke Tsohon Alkawali. AT: "yana karatu daga littafin Ishaya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)