ha_tn/act/07/47.md

1.0 KiB

da hannaye suka gina

Hannaye na nufin mutane. AT: "da mutane suka gina" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-synecdoche)

'Sama kursiyina ce, duniya kuwa wurin ajjiye sawayena ne

Shi annabin yana kwatanta girman darajar kasancewar Allah ne da yadda ba shi yiwuwa mutum ya gina wa Allah wurin da zai huta a duniya tun da shike duniyan gaba ɗaya wurin ajiye sawun sa ne kawai.

wane irin gida za ku gina mani?

Allah ya yi wannan tambayan ne domin ya nuna cewa aikin banza ne kokarin mutum ya kula da Allah. AT: "Ba za ku iya gina mani gida daidai yadda zai ishe ni ba!" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

ina ne wurin da zan huta?

Allah ya yi wannan tambayan ne don ya nuna cewa mutum ba zai iya tanada wa Allah wurin hutu ba. AT: "Babu wani wurin hutu da ya mani kyau!" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)

Ko ba hannayena ne suka yi dukan waɗannan ba?

Allah ya yi wannan tambayan ne don ya nuna cewa mutum bai halice kome ba. AT: "Hannayena ne suka yi dukan kome!" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-rquestion)