ha_tn/act/03/21.md

1.3 KiB

Shine wanda dole sama ta marabta

"shine wanda dole sama ta marabta." Bitrus yana maganar sama kamar wani mutum ne wanda ke marabtan Yesu zuwa gidansa. (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-personification)

dole sama ta karɓe shi har

Wannan na nufin cewa lallai ne Yesu ya cigaba da zama a sama domin abinda Allah ya shirya kenan.

har zuwa loƙacin komo da dukan abubuwa

Wannan na nufin 1) har zuwa loƙacin da Allah zai komo da dukan abubuwa 2) "har loƙacin da Allah zai cika komai da ya anabta."

game da abubuwan da Allah ya faɗa tun da ta bakin annabawansa tsarkaka

Da annabawa suka yi magana, yana kamar Allah ne da kansa ke maganan domin shi ne yake faɗa musu abinda za su ce. AT: "game da abubuwan da Allah ya yi magana da ta wurin cewa annabawansa tsarkaka su yi magana game da su"

ta bakin annabawasa tsarkaka

A nan kalmar "baki" na nufin maganganun da annabawa sun faɗa ko sun rubuto. AT: "maganganun dukan annabawansa tsarkaka" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

zai tayar maku da wani annabi kamar ni daga cikin 'yan'uwanku

"za sa ɗaya daga cikin 'yan'uwanku ya zama annabin gaskiya, kuma kowa zai san da shi"

'yan'uwanku

"kasanku"

za a hallakar da annabin nan gaba ɗaya

AT: "shi annabin, Allah zai hallakar da shi gaba ɗaya" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-activepassive)