ha_tn/3jn/01/05.md

1.2 KiB

Mahaɗin Zance:

Yahaya ya rubuta wannan wasiƙa ne domin ya yaba wa Gayus da yadda ya riƙe mallamai na Littafi masu tafiye tafiye; sai ya yi magana game da mutane biyu , ɗaya mai halin kirki da kuma ɗaya mai hali marar kirki.

Ya ƙaunatace

A nan ana amfani da kalmar ƙauna domin yan'uwa masubi.

kana aiki da aminci zuwa ga 'yan'uwa da baƙi

"kana aiki da aminci ga Allah" ko kuma "ka na biyayya da Allah"

yi wa 'yan'uwa da kuma baƙi

"taimaki 'yan'uwa masubi da waɗanda ba ku sansu ba"

baƙi, waɗanda suka shaida ƙaunar ka a gaban ikilisiya

"baƙi waɗanda suka faɗa wa masubi a cikin ikilisiya game da yadda ka ƙaunace su"

Zai yi kyau ka sallame su

Yahaya ya na gode wa Gayus domin taimako da ya saba yi wa waɗannan masubi.

domin sabili da sunan nan ne suka fito

A nan "sunan" na nufin Yesu. AT: "saboda sun fita domin su gayawa mutane game da Yesu" (Dubi: rc://*/ta/man/translate/figs-metonymy)

karɓa kome

babu karɓar kyauta ko kuma taimako

Al'umman

A nan "Al'umman" ba yana nufin mutane da ba Yahudawa kaɗai ba. Ya na nufin mutane da ba su dogara da Yesu ba.

domin mu zama abokan aiki tare da su a kan gaskiya

"domin mu hada kai da su a sanar da gaskiyar Allah ga mutane"